in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CRCC ya fara gwajin jiragen kasa a birnin Makka wanda ya kammala gabanin fara aikin hajjin bana
2018-06-21 09:53:51 cri
A jiya Laraba ne kamafin (CRCC) na kasar Sin ya fara yin gwajin jiragen kasa a birnin Makka gabanin fara aikin hajjin bana a watan Augasta a lokacin da miliyoyin maniyyata za su ziyarci kasa mai tsarki domin sauke farali

Kamfanin CRCC, wanda ya gudanar da aikin gina layin dogon a Makka, ya kara samun wani aikin kwangilar wanda ya kai kimanin kudin Riyal na kasar Saudiyya miliyan 350 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 93 wanda gwamnatin Saudi ta amince da aikin a watan Afrilu.

Kamfanin ya fara aikin gina layin dogo a kasar Saudiyya ne a karon farko a shekarar 2010-2014 bayan kammala aikin, an gudanar da tafiye tafiye kimanin sau miliyan 15 ba tare da samun wani hadari ba.

Titin jirgin kasan, wanda ya kasance aikin gina layin dogo na farko da kamfanin kasar Sin ya gudanar a yankin gabas ta tsakiya, zai taimaka wajen saukaka cunkoson ababen hawa a hanyoyin motar birnin a lokutan gudanar da aikin hajji, kuma zai saukakawa mahajjata wajen gudanar da zirga zirga kasancewar aikin ya hade yankunan birnin uku.

A shekarar 2009, kamfanin ya yi nasarar lashe tallar kwangilar da aka gudanar, wanda ya kai nisan kilomita 18.25 yana da tashoshi 9. Kamfanin ya kammala aikin ne cikin watanni 16. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China