Sanarwar ta ce, wadannan 'ya'yan sarauta 11 sun yi dandazo a bakin kofar gwamnatin jihar Riyadh, inda suka bukaci sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud da ya soke umurninsa na dakatar da biyawa 'ya'yan sarauta kudin ruwa dana lantarki. Kana kuma sun yi kokarin nemowa iyalin wani yarima tallafin kudi, wanda aka yanke masa hukuncin kisa saboda laifinsa na kashe fararen-hula. 'Yan sanda sun kama wadanna 'ya'yan sarautar Saudiyya saboda sun ki ficewa daga wurin, wadanda a yanzu haka ake tsare dasu a wani gidan kaso dake birnin Riyadh don jiran hukunci.
Sanarwar ta kuma ce, sarkin Saudiya wato Salman ya jaddada cewa, babu wanda ya fi karfin doka, wato, duk wanda ya aikata laifi ko keta doka, tilas ne a yanke masa hukunci.
Wannan shi ne karo na biyu da Saudiyya ta yi gagarumin kamu kan 'ya'yan sarautar kasar.(Murtala Zhang)