in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin musamman kasar Sin da jami'in Saudiyya sun tattauna kan batun yankin Gabas ta Tsakiya
2018-05-07 11:10:11 cri

Wakilin musamman na kasar Sin mai kula da batun yankin Gabas ta Tsakiya Gong Xiaosheng, wanda ke ziyara a kasar Saudiyya, ya yi shawarwari da wani jami'in gwamnatin kasar.

Yayin da yake ganawa da Jamal Aqeel, karamin jami'i mai kula da sashen harkokin siyasa da tattalin arziki na ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya, Gong Xiaosheng ya ce, yanzu yankin Gabas ta Tsakiya na cikin halin yamutsi, kuma a matsayinta na aminiyar kasashen da ke yankin, kasar Sin, ta na fatan kasashe masu ruwa da tsaki, za su daidaita sabani a siyasance, domin hanzarta sa aya ga hargitsin mai zubar da jini, a kokarin tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na Gabas ta Tsakiya. Ya kara da cewa, kasar Sin tana son ci gaba da taka rawa ta fuskar kara azama kan yin shawarwari domin sulhuntawa, a kokarin daidaita batutuwan dake haifar da sabani.

A nasa bangaren, Jamal Aqeel ya yi fatan kasar Sin za ta yi amfani da tasirinta da yake karuwa a duniya da kuma kyakkyawar huldar zumunci dake tsakaninta da kasashen yankin, wajen kara ba da gudummowa ga aikin shimfida zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya.(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China