in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiyya ta kakkabo makami mai linzami da aka harba zuwa Riyadh
2017-12-19 20:37:03 cri

Gamayyar rundunar dakarun da kasar Saudiyya ke jagoranta, ta bayyana cewa, ta yi nasarar kakkabo wani makami mai linzami da 'yan tawayen Houthi suka harba zuwa birnin Riyadh daga kasar Yemen.

A talatar nan ne dai gidan talabijin na Al Akhbariya, ya rawaito rundunar sojin saman kasar ta Saudiyya na tabbatar da aukuwar wannan lamari. Sai dai rundunar ta ce makamin bai haifar da wata barna ko lahanta wani ba. Kana makamin bai kawo wata tangarda ga zirga zirgar jiragen saman kasar ta Saudiyya ba.

'Yan tawayen Houthi dai sun sha hakon biranen kasar ta Saudiyya, inda suke kai masu farmaki da makamai masu linzami tun daga shekarar 2015.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China