in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rouhani ya bukaci Saudiya da ta daina takalar Iran
2017-11-09 09:43:34 cri
Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran ya bukaci kasar Saudiya da ta dakatar da abin da ya kira, manufofin tana takalar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Rouhani ya ce, kasarsa tana goyon bayan ci gaban kasashen dake yankin ciki har da kasar Saudiya, kuma hanya daya ta cimma wannan nasara, ita ce kasancewa 'yan uwan juna, abokai da kuma taimakawa juna.

Shugaban wanda ya bayyana hakan, yayin zaman majalisar zartaswar kasar na jiya Laraba, ya ce kuskure ne babban Saudiya ta yi tunanin cewa, kasashen Amurka da Isra'ila su ne kawayenta, amma ban da Iran.

Ya kara da cewa, al'ummar Yemen sun yi amfani da makamansu wajen kai hare-haren mayar da martini kan biranen kasar Saudiya, inda ya karyata zargin da Saudiya ke yi mata na tsoma baki a harkokin kasashen dake yankin, biyo bayan matakan da Iran din ta dauka na yaki da ayyukan ta'addanci a kasashen Iraki da Syria kamar yadda kasashen suka bukata.

Shi ma ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammed Javad Zarif, ya karyata zargin da yarima mai jiran gadon masarautar Saudiya Mohammed bin Salman ya yiwa Iran din a matsayin maras tushe kuma mai hadarin gaske.

Kafar talabijin ta Press ta ruwaito Zarif na cewa, yarima Salman yana zargin Iran da kai mata hari, wanda ya ce ya saba dokokin kasa da kasa da ka'idojin MDD. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China