in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiyya ta kakkabo makamai masu linzami biyu na dakarun Houthi
2018-04-24 11:04:34 cri

Kawancen sojojin kasa da kasa a karkashin jagorancin kasar Saudiyya ya bayyana jiya Litinin cewa, sojojin tsaron sararin sama na Saudiyya, sun kakkabo makamai masu linzami biyu da dakarun Houthi na kasar Yemen suka harba zuwa jihar Jazan da ke kudancin kasar ta Saudiyya.

A cikin sanarwar da kakakin kawancen sojojin Turki Al Maliki ya bayar, an ce, da misalin karfe 4 da mintoci 23 na yammacin ranar 23 ga wata ne, sojojin tsaron sararin sama na Saudiyya, suka yi nasarar kakkabo wadannan makamai masu linzami biyu. Ya ce ko da yake burbushin mamakan ya fada unguwannin fararen hula, amma ba wanda ya mutu ko ya ji rauni sakamakon hakan.

Bugu da kari kuma, dakarun Houthi na Yemen, sun bayyana ta gidan talibijin cewar, sun harba makamai masu linzami na wannan karo ne, domin lalata injunan man fetur na kamfanin man kasar ta Saudiyya da ke jihar Jazan.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China