in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin manzon musamman na shugaban Sin da Shugaban Afirka ta kudu
2018-03-24 12:47:27 cri
Manzon musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, wanda kuma shi ne mamban ofishin siyasar kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Yang Jiechi, ya gana da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa.

Yayin ganawar tasu a jiya Juma'a a birnin Capetown, Yang ya isar da sakon gaisuwa da fatan alheri da shugaba Xi ya aikewa Shugaba Ramaphosa, inda kuma ya yi bayanin irin muhimmancin da shugaban kasar Sin ke ba dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni dake tsakanin kasashen biyu. Yang ya kara da cewa, shugabannin kasashen biyu za su shugabanci taron kolin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda za a shirya a bana a birnin Beijing, yayin da kaasar Afirka ta kudu za ta karbi bakuncin taron tattaunawar shugabanni kasashen BRICS da za a shirya a Johnnesburg. A cewar Yang Jiechi, Kamata ya yi kasashen biyu su nuna goyon baya ga juna da nufin tabbatar da cimma nasarar manyan tarukan biyu.

A nasa bangaren, Cyril Ramaohosa ya bukaci Yang da ya isar da sakonsa na taya murnar zama shugaban kasa ga shugaba Xi Jinping. Baya ga haka, ya ce, kasarsa na fatan amfani da damar cika shekaru 20 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, wajen kara tuntubar juna da zurfafa hadin kai irin na samun moriyar juna. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China