Lauyoyin gwamnatin kasar da na wanda ake tuhuma, sun amince da neman dage sauraron shari'ar zuwa ranar 8 ga watan Yuni, wanda ya zo mintuna kalilan bayan Jacob Zuma ya gurfana na wani dan lokaci a gaban kotun, domin fuskantar tuhume-tuhume 16 da ake masa wadanda ke da nasaba da cin hanci da rashawa.
Jacob Zuma ya gabatar da jawabi ga dubban magoya bayansa da suka taro a wajen kotun, inda ya ce musu ba za a taba tabbatar da tuhume-tuhumen da ake masa ba.
Sai dai, jam'iyya mai mulkin kasar ANC ta kauracewa goyon bayan Zuma, tana mai cewa mutane za su iya goyon bayansa bisa kashin kansu, amma ba a matsayin mambobin jam'iyyar ba.
Ita ma jam'iyyar kwaminis ta kasar SACP, dake kawance da jam'iyyar ANC, ta nesanta kanta da shi. (Fa'iza Mustapha)