Da yake jawabi a taron dandalin shugabanni da masu ruwa da tsaki na jami'ar Sin da Amurka da aka gudanar a jami'ar Columbia, Kissinger ya jaddada cewa, rashin jituwa tsakanin kasashen biyu ba zai kasance mai fa'ida ga kasashen da ma duniya baki daya ba.
Ya ce, kasar Sin tana kokarin cimma wasu manufofi da babban sakataren JKS ya ayyana yayin zaman taron JKS karo na 18 da ya gudana a shekarar 2012. Kuma babu tantama kasar ta Sin za ta cimma wannan nasarar wadannan manufofi. (Ibrahim Yaya)