in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha: za a mayar da martani kan "cire tutar kasar Rasha" da kasar Amurka ta yi
2017-10-13 10:33:26 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova, ta bayyana cire tutocin kasarta a karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin San Francisco da ofishin kasuwancinta dake Washington DC da Amurka ta yi bisa radin kanta, a matsayin cin zarafi, inda Rasha ta yi suka da kakkausar harshe kan lamarin, tana mai cewa za ta dauki matakan mayar da martani.

A yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya, Madam Maria Zakharova ta bayyana cewa, Amurka ba ta samu izinin cire tutocin daga wajen Rasha ba. Kuma baya ga haka, Amurkar na neman takardun da Rasha ta ajiye a cikin wadannan hukumomi.

Zakharova ta kara da cewa, bisa yarjejeniyar diflomasiyya da kasashen Rasha da Amurka suka kulla, dukkan wadancan hukumomin diflomasiyya sun daina aiki, kuma bangaren Amurka ba shi da ikon samun wadancan takardu a ko yaushe kuma a ko'ina.

Bangaren Rahsa ya nemi bangaren Amurka ya mai da hankali kan ka'idojin daidaito da aka gindaya cikin tsarin diflomasiyya.

A ranar 2 ga watan nan ne, Rasha ta yi suka da kakkausar harshe bisa shiga karamin ofishin jakadancinta dake birnin San Francisco da ma'aikatan Amurka suka yi ba tare da samun izini ba.

Har ila yau, a ranar 11 ga wata ne Amurka ta cire tutocin Rasha da aka kafa a karamin ofishin jakadancin Rashar dake San Francisco da kuma ofishin kasuwancinta da ke Washington DC.

A ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata ne, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa, saboda Rasha ta nemi Amurka da ta rage yawan ma'aikatan hukumomin diflomasiyyarta dake kasar Rasha, ita ma Amurka ta nemi Rasha da ta rufe karamin ofishin jakadancinta dake San Francisco da wasu hukumomin diflomasiyya biyu dake Washington da New York kafin ranar 2 ga watan Satumba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China