in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a fito da dokoki game da yaki da cin hanci
2017-11-07 11:26:44 cri
Mahukuntan kasar Sin sun yi kira da a bullo da wani kundi wanda zai taimakawa kasashe wajen tsara dokoki game da dawo da kadarorin da aka sata.

Mai ba da taimako ga ministan harkokin wajen kasar Sin Qian Hongshan wanda ya yi wannan kira yayin taron kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa ta MDD, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su kara zurfafa hadin gwiwa a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa.

Mr Qian ya ce, yana da muhimmanci taron da ma kasashen da abin ya shafa su karfafa hadin gwiwa da musayar bayanai game da irin wadannan kadarori da ake sacewa. Koda yake jami'n na Sin ya ce, akwai wasu matsaloli da ake fuskanta a duk lokaci da ake maganar hadin gwiwa game da dawo da kadarorin da aka sata sakamakon wasu bambance-bambancen da suka shafi tsarin dokoki da wasu abubuwa tsakanin kasashe.

Ya ce kasar Sin ta gabatar da wasu shawarwari guda uku ta yadda za a karfafa hadin gwiwa a yakin da ake da cin hanci. Na farko karfafa tattaunawa kan yaki da cin hanci da rashawa bisa la'akari da inganci da irin alfalun da za a samu bayan an nazarci muradun bangarorin da abin ya shafa. Na biyu kara karfafa matakan yaki da cin hanci, ta hanyar kara karfin taron tare da warware banbance-banbancen dake tsakanin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasashe, sai na uku zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya yadda za a ci gajiyar sakamakon yaki da cin hancin. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China