in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen EU 14 sun kori jami'an diflomasiyyar Rasha, inda Rashar ta lashi takobin mayar da martani
2018-03-27 10:21:12 cri
Shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk, ya sanar da cewa, kasashen tarayyar 14 sun yanke shawarar korar jami'an diflomasiyyar Rasha, a wani mataki na mayar da martani ga sanya guba ga tsohon jami'in liken asirin Rasha da 'yarsa a garin Salisbury na Birtaniya.

Donald Tusk ya bayyanawa manema labarai jiya a birnin Varna na Bulgaria cewa, a makon da ya gabata, majalisar EU ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da aka kai Salisbury, kuma majalisar ta amince da gwamnatin Birtaniya da ke ganin akwai alamu masu karfi dake nuna gwamnatin Rasha ce ke da alhakin sanya gubar, kuma babu wani kwakkwaran bayanin da ya sabawa hakan.

A jiya Litinin ne ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce kasarta na adawa da korar jami'anta da Amurka da wasu kasashe 14 na Tarayyar Turai suka yi kan tsohon jami'in liken asirin, tana mai alkawarin kasarta za ta mayar da martani.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce an dauki matakin a matsayin kiyayya, wanda kuma bai dace da muradin gudanar da binciken musababbi da wadanda ke da hannu wajen sanyawa jami'in guba a ranar 4 ga watan nan ba.

Sanarwar da ta musanta hannun Rasha cikin batun, ta ce hukumomin Birtaniya sun dauki matsayar nuna tsana da wariya da munafunci. (Fa'iza Musatapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China