in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano kwayar halittar gado mafi tsufa a Morocco
2018-03-16 11:13:07 cri
Ma'aikatar kula da harkokin al'adu ta kasar Morocco ta sanar a jiya Alhamis cewa, an gano wata kwayar halittar gado mafi tsufa a makabartar Grotte des Pigeons kusa da garin Taforalt dake gabashin kasar.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce gano kwayar halittar gadon wadda ake ganin za ta kai shekaru 15,000, zai kara samar da wasu sabbin bayanai game da tarihin bil-Adama a duniya. Sanarwar ta kara da cewa, tarihin dai-daikun mutane,na zamanin amfani da duwatsu, ya yi kama da al'ummomin da suka zauna a gabashin duniya da wani bangare na al'ummomin Afirka dake yankin kudu da hamadar sahara.

Wannan wani gagarumar nasarar ce da masu binciken kayan tarihi na karkashin kasa suka samu a kasar ta Morocco a baya-bayan nan. Ko da a watan Yunin da ya gabata ma, wata tawagar masana kimiya ta duniya ta gano wani kwarangwal na bil-Adama a kauyen Jbel Irhoud dake kusa da gabashin birnin Youssoufia, wanda aka yi imanin shi ne kwarangwal mafi tsufa a duniya.

A cewar cibiyar kimiyar kayayyakin tarihi ta kasar Morocco, kwarangwal din na iya kaiwa sama da shekaru 300,000. Abin da mayar da asalin shekarun bil-Adama baya da shekaru 100,000, har tana ganin cewa, ba a gabashin Afirka kadai aka fara samun asalin bil-Adama ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China