Dandalin, wanda kungiyar sada zumunta tsakanin jama'ar kasar Sin da kasashen waje ta Sin ta shirya, gami da hadin gwiwar kungiyar mu'amalar sada zumunci tsakanin Morocco da Sin na da taken 'Morocco, mashigar shawarar ziri daya da hanya daya ta kasar Sin a nahiyar Afirka.'
Mataimakiyar shugaban kungiyar sada zumunta tsakanin jama'ar kasar Sin da kasashen waje ta Sin, Lin Yi, ta ce, akwai dadadden zumunci tsakanin Sin da Morocco, kana, a matsayin membar kungiyar tarayyar Afirka, da ta kawancen kasashen Larabawa, Morocco za ta iya kara taka muhimmiyar rawa a fannoni da dama, ciki har da fadada hadin-gwiwa, da raya kyakkyawar hulda tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da kasashen Larabawa, musamman ma wajen aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya'.
An kafa dandalin tattaunawa don karfafa zumunci tsakanin Sin da Morocco ne da nufin kara samun fahimtar juna tsakanin birane da jihohin kasashen biyu, da inganta hadin-gwiwarsu a fannonin kasuwanci da al'adu, da kuma yawon shakatawa.(Murtala Zhang)