Da yake karin haske kan hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ministan harkokin wajen kasar Morocco Nasser Bourita, ya ce kasarsa za ta kori jakadan kasar Iran dake Morocco sannan ta rufe ofishin jakadancinta dake Tehran, saboda yadda Iran din take goyon bayan kungiyar 'yan awaren Polisario dake yammacin Sahara.
Ministan ya ce, kasarsa tana da kwararan shaidu game da hannun kasar Iran ta abokanta Hezbollah dake kasar Lebanon, inda take goyon bayan sojojin Polisario ta yadda take horos da mambobin kungiyar domin ta kawo illa ga tsaro da zaman lafiyar Morocco.
Bourita ya ce, tuni ya mikawa takwaransa na kasar Iran wadannan shaidu, wadanda suka hada da muhimman takardu kan yadda aka mikawa kungiyar 'yan tawayen makamai. (Ibrahim Yaya)