Bikin wanda ya kasance karo na 55, wanda AU ta gudanar a helkwatar kungiyar dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, an shirya tarukan tattaunawa, kana an yi bikin nune nunen al'adun gargajiya na kasashen Afrikan.
Da yake karanto wasu daga cikin nasarorin da Afrikar ta cimma a lokacin bikin, shugaban gudanarwar kungiyar ta AU, Moussa Faki Mahamat, ya jaddada bukatar daukar matakan da suka dace da kuma yin takatsantsan don kaucewa abubuwan da za su iya dakile cigaban nahiyar. Shugaban ya ce babban aikin dake gabansu shi ne yaki da duk wani nau'in rashawa, inda ya nanata cewa, ayyukan rashawa ka iya rusa rayuwar dukkan talakawa da kuma haifar da rashin yarda a tsakanin talakawan da shugabanninsu, har ma da kawo barazana ga cigaban hukumomi da ma'aikatan gwamnati a fadin nahiyar.
AU ta ware shekarar 2018 a matsayin shekarar yaki da rashawa, inda ta baiwa babban taron kolinta taken "Yin galaba a yaki da rashawa: Shi ne hanyar samar da dawwamamman cigaban nahiyar Afrika", kana shugabannin Afrika sun kebe ranar 11 ga watan Yuli a matsayin ranar yaki da rashawa a Afrika.
An bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin jagoran yaki da rashawa na Afrika, bisa la'akari da kokarin da gwamnatinsa ke yi na yaki da rashawa a Najeriya da ma duniya baki daya. (Ahmad)