Daraktan hukumar wayar da kai ta kasar (NOA) Musa Shantu, ya bayyana jiya a Abuja babban birnin kasar cewa, za a gudanar da shirin ne a yankunan Maiduguri da Goza na jihar Borno.
Ya ce wayar da kan ya zama wajibi duba da yadda wadanda suka tuba, kuma suka shiga shirin gyaran hali, kana suka shirya komawa cikin al'ummominsu ke fuskantar kalubale.
Musa Shantu, ya ce komawa cikin al'umma ya zama abu mai wahala ga galibinsu, la'akari da yadda al'ummomin ke da mummunan tunani kansu.
A cewarsa, hukumar NOA za ta tattauna da jama'a domin tabbatar musu cewa mayakan da suka tuba, sun canza tare da sauya hali. (Fa'iza Mustapha)