Kafar yada labarai ta PR Nijeriya, wadda ke shirya sanarwa ga hukumomin tsaro, ta ruwaito cewa, daga cikin wadanda aka sace akwai wata mace da jaririyarta.
Matafiyan na tafiya ne a kan titin nan mai hadari na Birnin-Gwari dake Kaduna, a lokacin da 'yan bindigar suka tsaida su a kwanar-tsauni, dake tsakanin kauyukan Udawa da Labi dake yankin.
Wani direban motar haya da al'amarin ya auku kan idonsa mai suna Mohammed Kebi, ya ce a kalla motoci 5 masu satar mutanen suka tsare da misalin karfe 11 na safiyar jiya Jumma'a.
Shi ma wani ganau Musa Yakubu, ya ce titin na Birnin-Gwari ya zama inda masu satar mutane don neman kudin fansa ke cin karensu ba-babbaka.
Tun daga farkon shekarar nan, an samu gomman hare-hare a yankin na arewa maso yammacin Nijeriya, duk da kokarin da gwamanatin kasar ke yi na ganin ta kawo karshen al'amarin. (Fa'iza Msuatpha)