in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya zai ziyarci Morocco
2018-06-10 09:37:08 cri

A yau Lahadi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa kasar Morocco don amsa goron gayyatar da sarki Mohammed VI ya yi masa, ministan kula da harkokin masarautun kasar Morocco ne ya bayyana hakan a jiya Asabar.

Sanarwar ta ce, bangarorin biyu za su gudanar da tattaunawa a hukumance, ya kara da cewa, wannan ziyarar tana kara bayyana yadda kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu take shafar hadin gwiwa a tsakanin kasashen, da irin burin da suke son cimmawa wajen kulla alaka a fannoni masu yawan gaske.

Dangantaka tsakanin Morocco da Najeriya tana kara samun kyautatuwa musamman a 'yan shekarun da suka gabata.

A lokacin da sarkin Morocco ya ziyarci Najeriya a watan Disambar 2016, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin shimfida bututan iskar gas wanda zai hade kasashen na yammacin Afrika.

Aikin shimfida bututan zai ratsa kasashen yammacin Afrika masu yawa, kana zai iya ketarwa zuwa Turai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China