in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta sauka zuwa matsayi na 48 a jerin kasashe mafiya kwarewa wajen taka leda na hukumar FIFA
2018-06-08 13:20:05 cri

Kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles, ta yi kasa zuwa matsayi na 48, a jerin kasashe mafiya kwarewa a fannin buga kwallo, cikin jadawalin da hukumar FIFA ta fitar a baya bayan, gabanin bude gasar cin kofin duniya da ake daf da farawa a Rasha. Najeriyar ta kuma sauka zuwa matsayi na 7 a nahiyar Afirka a jadawalin na FIFA.

Kafin hakan Super Eagles na matsayi na 47 a duniya, da kuma na 6 a Afirka cikin jadawalin da FIFAr ta fitar a watannin Afrilu da Mayun wannan shekara.

Bayanai daga shafin yanar gizo na hukumar ta FIFA ya nuna cewa, hukumar ta kai ga fidda sakamakon karshe na matsayin kungiyoyin kasashen ne, bisa rawar da suka taka a wasannin su na sada zumunta.

Czech Republic ta doke Super Eagles ta Najeriya da ci daya da nema, a wasan sada zumunta da suka buga a ranar Laraba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China