Kasashen duniya sun nuna goyon bayansu ga yarjejeniyar nukiliyar ta Iran, in ban da Irsra'ila da wasu tsirarun kasashen Larabawa inda suka goyi bayan Amurka, yarjejeniyar wacce aka fi sani da (JCPOA).
An jiyo Zarif yana jawabi ta gidan talabijin din kasar yana cewa, sun yi amanna har yanzu kasa da kasa suna goyon bayan yarjejeniyar ta JCPOA, sai dai shugaban kasar Amurka Donald Trump bai sauya matsayinsa game da sharrudan da ya gindaya ba.
Ya nanata cewa, sun yi amanna da kasarsu, kuma hakan shi ne ke baiwa kasarsu kwarin gwiwa a matsanancin halin da ake ciki game da warware takaddamar shirin nukiliyar ta Iran. (Ahmad Fagam)