Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO, ta fara gudanar da wani gangamin dakile yaduwar cutar na gida gidan a birnin Mubi, domin sada masu dauke da ita da tallafin jami'an lafiya.
Jami'in dake lura da shirin Kabiru Sadiq, ya ce matakan gaggauwa da ake dauka sun bada damar gano sabbin masu kamuwa da cutar, wanda hakan ke kare mummunan tasirin da take da shi na hallaka al'umma. Ya ce yanzu haka yawan masu rasuwa sakamakon kamuwa da Cholera ya ragu daga kaso 17 bisa dari zuwa kaso 1.7 bisa dari. (Saminu)