in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaiwa sansanonin sojan Syria hari da makami mai linzami
2018-04-30 15:24:44 cri
Rahotanni daga kasar Syria na cewa, an kaiwa sansanonin sojojin kasar dake wajen lardunan Hama da Aleppo hari da makami mai linzami.

Koda ya ke babu karin bayani game da wanda ya kai harin, amma gidan talabijin na kasar ya nuna hotunan yadda wuta ke tashi a wurin da aka kai harin. An dai kaiwa sansanonin sojan kasar Syria dake wajen lardunan Hama da Aleppo sabon harin ne da misalin karfe 10 da rabi agogon wurin.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, an kaiwa bataliyar soja ta 47 dake Hama hari, lamarin da ya haddasa babbar gobara da karar fashewa yayin da su ma sojojin Syria suka mayar da martani ga harin makamai masu linzamin.

A halin da ake ciki kuma, hukumar dake sanya ido kan kare hakkin bil-Adama ta Syria, ta ce mayakan Iran da wasu 'yan adawa dake yankin na da hannu a harin, inda ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa cibiyoyin Sojan Syria dake lardin na Hama.

Duk da cewa, har yanzu babu wani karin bayani game da sabon harin da aka kai, harin makami mai linzami na zuwa ne yayin da sojojin na Syria suka fatattaki dakarun Syria da Amurka ke marawa baya (SDF) a yankunan dake wajen lardin Deir al-Zour na gabashin Syria.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne dai kasashen Amurka da Burtaniya da Faransa suka kaddamar da jerin hare-haren makamai masu linzami kan sansanonin sojan Syria, domin mayar da martani kan zargin da ake yiwa gwamnatin Syria da kai hari da iskar gas mai guba kan tsohon yankin da ya fada hannun 'yan tawaye a gabashin Damascus. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China