Kungiyar tarayyar Turai da MDD ne suka shirya taron tare, kuma wakilan da suka fito daga kasashe da kungiyoyin duniya 85 ne suka halarci taron. A yayin bikin bude taron, babbar wakiliyar kungiyar tarayyar Turai mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro, ta yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su koma teburin shawarwari, don cimma wani shiri na daidaita matsalar Syria a siyasance.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu yakin Syria ya haifar da barazana ga kwanciyar hankalin shiyyarta, da ma duniya baki daya. Ya ce, zai ci gaba da tuntubar mambobin MDD, don gano bakin zaren warware matsalar bisa kuduri mai lambar 2254, na kwamitin sulhun MDD da kuma sanarwar Geneva. (Lubabatu)