A jawabin da ya gabatar a gun taron, Mr. Xie Xiaoyan ya gabatar da shawarwari guda uku, wato na farko a tsaya ga yin shawarwari, na biyu kuma a tabbatar da tsagaita bude wuta, na uku, ya kamata kasa da kasa su hada karfinsu a kan batun.
Mr.Xie Xiaoyan ya kuma kara da cewa, sau da dama kasar Sin ta samar da gudummawar kayayyaki, da kudi cikin gaggawa ga al'ummar Syria, ciki har da 'yan gudun hijira da ke kasashen ketare, gudummawar da kawo yanzu ta kai kudin Sin yuan miliyan 740. A gaba, kasar Sin za ta gaggauta cika alkawuranta na samar da agajin jin kai, za ta kuma karfafa gwiwar kamfanonin kasar, ta yadda za su shiga aikin farfado da Syria muddin dai za a iya tabbatar da tsaronsu.(Lubabatu)