in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi jawabi a matsayin shugaban kasar dake daukar bakuncin taron SCO
2018-06-11 10:17:17 cri

A jiya Lahadi ne, shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO suka gana da 'yan jarida, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a matsayin shugaban kasar dake daukar bakuncin taron na SCO.

Xi Jinping ya yi bayani game da batutuwan da aka cimma daidaito da sakamakon da aka samu a yayin taron kolin kungiyar SCO na Qingdao, wato bangarori daban daban su amince su kara hada kai, da zurfafa hadin gwiwarsu cikin lumana, da nuna wa juna adalci, bude kofa da fahimtar juna da kuma samun moriya tare.

Bangarorin su kuma martaba ra'ayin samar da dauwamammen zaman lafiya da tsaro cikin hadin gwiwa a yankin. Kana za su tabbatar da 'yancin ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya, da tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban bisa tushen bude kofa da fahimtar juna da nuna adalci da kuma bin ka'idoji, da kin amincewa da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya ta kowace hanya, da kara gudanar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da ci gaba da yin hadin gwiwa a fannonin al'adu, ba da ilmi, kimiyya da fasaha, kiyaye muhalli, kiwon lafiya, yawon shakatawa, matasa, kafofin watsa labaru, wasanni da sauransu, da sa kaimi ga yin mu'amala a fannin al'adu a tsakanin jama'a. Hakazalika, za a fadada hadin gwiwa a tsakanin kungiyar SCO da sauran kasashen duniya, da hada kai da MDD da sauran hukumomin kasa da kasa da yankuna wajen ganin an samu zaman lafiya da wadata tare, da nuna goyon baya ga kasar Kyrgyzstan don daukar bakuncin taron koli na kungiyar a badi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China