in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin: Hadin gwiwar Sin da Rasha zai kawo alfanu ga bunkasuwar dangantakar kasa da kasa
2018-06-11 09:59:02 cri

A jiya ne, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya shedawa manema labarai cewa, hadin kai tsakanin Sin da Rasha ya kai ga kyakkyawan matsayi, don haka ya kamata a kara bunkasa shi, saboda ba ma kawai zai kawo alfanu sosai ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu ba, zai yi babban tasiri ga bunkasuwar dangantakar kasashen duniya.

Yayin da ya tabo batun ci gaban da aka samu a kungiyar SCO da makomar wannan kungiya kuwa, Putin ya bayyana cewa, ban da batun yaki da ta'addanci da tsaro da aka tattauna a wannan taro, bangarori daban-daban mahalarta taron su kuma nanata wajibcin nacewa ga martaba ka'idar ciniki ta duniya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China