in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Iran za su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu
2018-06-11 09:42:04 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Iran Hassan Rouhani, a jiya Lahadi sun cimma matsaya na karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Shugabannin biyu sun cimma matsaya ne a lokacin taron kolin Shanghai na hadin gwiwar kasashe mambobin kungiyar SCO karo na 18 wanda ya gudana a birnin Qingdao, dake lardin Shandong na gabashin kasar Sin.

Da yake bayyana muhimmancin warware takaddamar nukiliyar kasar Iran a matsayin muhimmin batu da zai baiwa kasar damar yin hulda da kasa da kasa, shugaba Xi ya ce, yarjejeniyar nukiliyar zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da samun kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya har ma da batun kawar da barazanar makamai masu guba a tsakanin kasa da kasa, kana za'a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

A ko da yaushe kasar Sin tana kan matsayinta na wanzar da zaman lafiya, da warware rikice rikice a kasa da kasa, da magance duk wasu batutuwa da suka shafi tashe tashen hankula, kana a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da Iran karkashin tsarin kasa da kasa, da kuma gina sabon tsarin yin cudanya da dangantakar kasa da kasa, in ji Xi.

Batun yarjejeniyar nukiliyar Iran yana fuskantar kalubaloli a halin yanzu, kuma kasar Iran tana bukatar taimakon al'ummar kasa da kasa ciki har da kasar Sin, domin su taka muhimmiyar rawa wajen warware takaddamar da ta shafi nulikiyar kasar, in ji Rouhani. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China