in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#Taron SCO#Xi Jinping: An cimma matsaya daya a wajen taron kolin Qingdao na kungiyar SCO
2018-06-10 15:30:46 cri
Yayin da yake ganawa da manema labarai tare da takwarorinsa na kasashe membobin kungiyar hadin-kai ta Shanghai ko kuma SCO a takaice, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, shugabannin kasashe membobin kungiyar da na kasashe 'yan kallo tare kuma da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya sun yi musanyar ra'ayoyi kan wasu muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, inda suka cimma matsaya a fannoni da dama. Haka kuma, an fitar da sanarwar Qingdao ta majalisar shugabannin kasashe membobin kungiyar SCO, da hadaddiyar sanarwa kan saukaka harkokin kasuwanci ta shugabannin kasashe membobin kungiyar SCO, gami da amincewa da manufofin zartas da yarjejeniyar karfafa dankon zumunci da hadin-gwiwa cikin dogon lokaci tsakanin kasashe membobin kungiyar SCO nan da shekaru biyar masu kamawa.(Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China