in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco tana fatan samun masu yawon shakatawa dubu dari 5 daga Sin nan da shekarar 2020
2018-02-02 11:06:55 cri
Jiya Alhamis, a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar harkokin yawon shakatawa a tsakanin kasar Sin da kasar Marocco da aka yi a birnin Casablanca na kasar Morocco, minista mai kula da harkokin yawon shakatawa, sufurin jiragen sama, sana'ar hannu da tattalin arziki da zamantakewar al'umma na kasar Morocco Mohamed Sajid, ya bayyana cewa, suna fatan ya zuwa shekarar 2020, adadin masu yawon shakatawa wadanda suka fito daga kasar Sin zuwa kasar Morocco za su kai dubu dari 5.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, ana tattaunawa kan bude hanyar sufurin jiragen sama daga kasar Morocco zuwa kasar Sin kai tsaye, wannan shi ne babban matakin kasar Morocco wajen kara janyo hankulan masu yawon shakatawa na kasar ta Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China