Da yake gabatar da jawabi, Xi Jinping, ya ce yana farin cikin ganinsu a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabar rawayan teku.
Ya kara da cewa, a madadinsa da gwamnati da al'ummar kasar Sin, yana yi wa dukkansu maraba, musammam Shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da suka halarci taron majalisar shugabannin kasashe mambabin SCO. (Fa'iza Mustapha)