in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashen Pakistan da Uzbekistan
2018-06-09 20:07:07 cri
A Yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain a birnin Qingdao.

Shugaba Hussain ya bayyana cewa, kasarsa tana tsayawa tsayin daka wajen kare manufar "kasar Sin kasa daya tak" a duniya, da kuma dukufa wajen kiyaye babbar moriyar Sin, domin tana son ci gaba da mu'amalar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu, yayin da kuma take karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, a fannonin tattalin arziki, ciniki da kuma kara tsaron kasa da dai sauransu.

A yayin da yake ganawa da shugaban kasar Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev, shugaba Xi Jinping ya ce, cikin 'yan shekarun nan, ana ci gaba da zurfafa huldar abota dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, kuma a halin yanzu, ana aiwatar da ra'ayoyi iri daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yadda ya kamata. Kasar Sin tana son ci gaba da karfafa zumuncin dake tsakaninta da kasar Uzbekistan, ta yadda za su nemi ci gaba cikin hadin gwiwa.

A nasa bangare kuma, Shavkat Mirziyoyev ya ce, kasarsa tana tsayawa tsayin daka wajen kiyaye manufar "kasar Sin kasa daya tak", kuma tana goyon bayan kasar Sin kan aikin "yaki da bangarori uku", wato yaki da 'yan ta'adda da yaki da masu neman ballewa da kuma yaki da masu tsattsauran ra'ayi. Haka kuma, ya ce, kasar Uzbekistan na son karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa shirin "Ziri daya da hanya daya", da kuma karfafa mu'amalar dake tsakaninsu kan harkokin yankin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China