Ma Zhaoxu ya yi wannan bayani ne yayin taron kasashen duniya kan hakkokin dan Adam da samar da kyakkyawar makoma na bai daya, wanda cibiyar kare hakkin dan Adam ta kasar Sin da shirin kasar Sin na MDD a Geneva suka shirya.
A cewar babban jami'in, samar da daidaito tsakanin yankuna shi ne tubalin inganta kare hakkin dan Adam, kuma dole ne dukkan bangarori su kare hakkokin dan Adam tare da tabbatar da hadin kai a matsayin 'yan uwan juna da kuma yi wa manufofin kare hakkokin dan Adam na sauran kasashe kyakkyawar fahimta.
Ma ya kuma jadadda muhimmanci damawa da kowa tare da koyo daga juna yana mai cewa ita ce muhimmiyar hanyar kare hakokin bil'adma.
Har ila yau, ya ce kamata ya yi al'ummomin duniya su girmama bambancin wayewar kan bangarori daban-daban ta yadda zai tafi kafada-da-kafada da zaman lafiya tare da koyi da juna. (Fa'iza Mustapha)