in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya amince da shekaru mafi karanci na wadanda ke neman shugabancin kasar
2018-06-01 15:14:37 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya amince da shekaru mafi karanci ga wanda ke neman takarar shugabancin kasar.

Muhammadu Buhari mai shekaru 75, ya rattaba hannu kan kudurin dokar ba matasa damar yin takara da ake wa lakabi da 'Not Too Young to Run Bill' jiya Alhamis a Abuja babban birnin kasar. Al'amarin da zai ba 'yan kasar masu shekaru 35 damar neman takarar shugabancin kasar.

Majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar ne a watan Yulin 2017, domin gyara wani sashe na kundin tsarin mulkin kasar, da nufin rage shekarun cancantar neman ofishin shugaban kasa daga 40 zuwa 35.

Shugaba Buhari, ya ce ya amince da kudurin ne saboda shi ne abun da matasa ke buri, domin samun cikakkiyar damar shiga harkokin siyasa a kasar.

Sabuwar dokar ta kuma rage shekarun neman zama mamban majalisar dokokin jihohi da na tarayya daga 30 zuwa 25.

Shugaban ya yi kira ga matasan Nijeriya su zama masu basira da dogaro da kai a loakcin da suka kama madafun iko.

Muhammadu Buhari, wanda tsohon Soja ne, kuma tsohon shugaban kasa na mulkin soji, zai sake tsayawa takara a wa'adi na biyu a badi. Nijeriya dai, za ta gudanar da babban zabenta ne a watan Fabrerun 2019. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China