in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta nemi a karfafa dangantaka a yammacin Afrika domin magance matsalar tsaro
2018-06-01 10:07:17 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira da a karfafa hadin kai a yankin yammacin Afrika domin magance barazanar tsaro da ke karuwa.

Muhammadu Buhari ya yi kira da a kara ingantawa tare da ci gaba da ayyukan tsaro, yana mai gargadin cewa, yaki a tare ne kadai zai dakatar da barazanar da mutane da dukiyoyi ke fuskanta.

Shugaban ya bayyana haka ne jiya a Abuja, babban birnin kasar, lokacin da ya karbi wasikar tura jakadan Mali a Nijeriya Moustapha Traore.

Shugaba Buhari ya ce yankin zai ci gaba ne da fafutukar neman ci gaba, muddun mutane su ka ci gaba da rayuwa cikin fargaba.

Ya ce ayyukan ta'addanci da na bata gari na karuwa a kasashen yankin, kuma suna iyakar kokarin kare rayuka da dukiyoyi, amma kuma sun raina wa tasiri da zirga-zirga tsakanin iyakoki ke da shi.

A nasa bangaren, Jakadan ya ce zai yi aiki tukuru wajen karfafa dangantakar kasashen biyu, a fannonin musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaron kasashen, da kuma batutuwan da suka shafi cinikayya da ci gaban tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China