in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kama manyan motoci dauke da albarusai dubu 300
2018-06-01 09:29:18 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, dakarun kasar sun yi nasarar kama wasu manyan motoci gudu uku a yankin Igbogila-ilara dake jihar Ogun a yankin Kudu maso yammcin kasar, makare da harsashe na zahiri sama da dubu 300.

Babban Kwamandan runduna ta 81 ta sojojin Najeriya, Manjo janar Enobong Udoh ya shaidawa manema labarai a Legas cibiyar kasuwancin kasar cewa,, an kama manyan motocin ne a kauyen Balogun a ranar Laraba. Ya ce, an boye harsashen ne a cikin wasu akwatuna da katon-katon na katako.

Kwamandan ya ce, direbobin da yaran su sun gudu sun bar motocin a lokacin da suka hango sojojin. Kuma yanzu haka suna kokarin zakulo direbobin da suka gudu da ma wadanda suka saka su wannan aikin.

Manjo-Janar Enobong ya ce, sun yi nasarar kama motocin ne, sakamakon bayanan sirrin da suka samu daga wasu 'yan Najeriya masu kishi. Ya kuma godewa mazauna jihohin Legas da Ogun dake yankin kudu maso yammacin kasar kan hadin kan da suke ci gaba da ba su, inda ya yi kira a gare su da su rika baiwa jami'an tsaro muhimman bayanai a kan lokaci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China