in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya
2018-04-27 19:58:27 cri
A yau Juma'a da yamma ne a birnin Wuhan, hedkwatar lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi wanda ke ziyara da kashin kai a kasar Sin, har ma shugabannin biyu suka kalli bikin nune-nunen kayayyakin tarihi da aka shirya a dakin adana kayayyakin tarihi na lardin Hebei.

Da farko dai, shugaba Xi Jinping ya nuna maraba da ziyarar da Modi ya kawo birnin Wuhan. Yana mai cewa, a cikin shekaru 3 da suka gataba, shi da firaminista Modi sun ziyarci juna, kana sun sha ganawa da juna a wurare daban daban. Ya zuwa yanzu sun kulla kyakkyawar dangantaka a hukumance a tsakaninsu, har ma sun cimma matsaya kan batutuwa da dama a yayin da kasashen biyu ke kara sada zumunta a tsakaninsu. Shugabannin biyu sun kuma bayyana yadda kasashen Sin da Indiya, wato kungiyoyin tattalin arziki masu muhimmanci sosai a duniya suke yin hadin gwiwar cin gajiya tare domin neman ci gaba tare. Idan kasaitattun kasashen biyu sun yi hadin gwiwa, tabbas za su yi tasiri mai muhimmanci a duniya baki daya. Mr. Xi na fatan ganawarsa da firaminista Narendra Modi za ta bude wani sabon shafin bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Indiya.

A nasa bangaren, Mr. Modi ya nuna godiya ga gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa ta yin ganawar kashin kai tsakaninsu a birnin Wuhan. Mr. Modi ya ce, tabbas wannan ganawa ce mai ma'ana a tarihi. Idan har kusoshin kasashen Indiya da Sin suka ci gaba da yin mu'amala da musayar ra'ayoyi a tsakaninsu, tabbas za a kara fahimtar juna da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, har ma ya dace da moriyar kasashen biyu, da ma yankin da kasashen biyu suke ciki. Bangaren Indiya na fatan hada kai da bangaren Sin domin cimma wannan buri.

Shugabannin kasashen biyu sun fara ganawa ne a dakin adana kayayyakin tarihi na lardin Hubei. A yayin da shugabannin biyu suka kalli al'adu mai dadadden tarihi na kasar Sin, musamman al'adun yankin Jin da Chu, sun kuma yi musayar ra'ayoyi kan yadda kasashen Sin da Indiya, wato tsoffin kasashe masu dadadden tarihin wayin kai za su kara yin ma'amalar al'adu ta yadda za a tabbatar da ganin al'adu daban daban za su iya zaman tare cikin lumana. Shugabannin biyu sun ci gaba da yin shawarwari a otel din tafkin Donghu.

Kamar yadda gwamnatocin kasashen Sin da Indiya suka tsaida, shugaba Xi Jinping da firaminista Modi za su yi shawarwari na kashin kai a birnin Wuhan daga yau Jumma' zuwa gobe Asabar 28 ga wata, inda za su yi musayar ra'ayoyi kan babban sauyin da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 100 da suka gabata a fadin duniya, har ma da batun yadda za a bunkasa dangantaka daga dukkan fannoni a nan gaba tsakanin kasashen biyu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China