in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta bukaci kasashen Afrika su kafa asusun tinkarar sauyin yanayi
2018-04-10 11:02:48 cri

Kenya ta bukaci kasashen Afrika su kafa asusun tinkarar sauyin yanayi domin ceton nahiyar daga karawa tattalin arzikinsu nauyi.

A cewar daraktan kula da sauyin yanayi na ma'aikatar muhalli ta Kenya Charles Mutai, asusun zai taimaka wajen samar da kudi domin tinkarar muhimman abubuwan da suka shafi sauyin yanayi.

Ya ce karuwar matsalolin sauyin yanayi na karawa nahiyar nauyi, a don haka akwai bukatar samar da asusu tara kudi na nahiyar.

Ya ce kudin zai taimaka wajen gaggauta samun ci gaba da yayata fasahohin dake da alaka da yanayi da makamashi mai tsafta a nahiyar.

Mutai ya bayyana cewa, Kenya ta samar da asusun tinkarar sauyin yanayi da dabarun kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire da za su taimaka wajen samun ci gaba da kuma tantance nasarorin da kasar ta samu a fannonin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China