Daniel Pennock, shugaban shirin bada horo kan yanayin kasa a tsakanin gwamnatoci wato (ITPS) karkashin shirin hukumar samar da abinci ta MDD (FAO), ya ce lokaci ya yi da ya kamata a gudanar da binciken domin hakan zai taimaka wajen kiyaye samar da abinci da kare muhalli da kuma lafiyar bil adama sakamakon karuwar da ake samu a tsarin bada kariya ga tsirrai wato (PPP) a takaice. Pennock ya furta hakan ne a lokacin bibiyar rahoton babban taron MDD kan kare muhalli (UNEA) wanda ake gudanarwa a halin yanzu a Nairobi.
Ya ce kasancewa kaso 95 bisa 100 na abinci ana samunsa ne daga kasa, don haka yana da matukar muhimmanci a kula da lafiyar kasa, domin samar da abinci mai lafiya wanda zai inganta lafiyar mutane da dabbobi baki daya. (Ahmad Fagam)