in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka sun lashi takwabin koyon fasahohin kare muhalli daga Sin
2017-12-06 09:48:55 cri

Shugaban taron ministocin kare muhalli na nahiyar Afirka (AMCEN) Pacome Moubelet-Boubeya ya bayyana kudurin kasashen nahiyar na koyon kyawawan dabarun kare muhalli na kasar Sin, domin rage yadda ake sare dazuka da gurbata iska a nahiyar.

Da yaka karin haske kan wannan batu yayin ganawa da manema labarai a birnin Nairobin kasar Kenya, Pacome ya ce, kasashen nahiyar na kuma shirye-shiryen aro managartan dabarun kare muhalli da rage gurtabar iska na kasar Sin, a wani mataki na kare nahiyar daga matsalar da take fuskanta a wadannan fannoni.

Moubelet-Boubeya wanda har ila shi ne ministan kula da gandun daji, koguna da muhalli na kasar Gabon, ya ce, nahiyar tana shirin kulla hadin gwiwa a fannin magance matsalar canjin yanayi, inganta matakan kiwon lafiya da yaki da fatara.

Jami'in ya kuma yaba wa matakai da taimakon da Sin take baiwa kasashen nahiyar, yana mai cewa, a matsayinsu na mambobin kungiyar kasashe masu tasowa, nahiyar Afirka tana fatan yin koyi da kasar Sin, domin inganta tattalin arziki da jin dadin al'ummominta, kamar yadda hakan ke kunshe cikin ajandar samar da ci gaba ta duniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China