in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron MDD kan muhalli da alkawarin kawo karshen gurbatarsa
2017-12-07 10:12:26 cri

An kammala kashi na 3 na taron MDD kan muhalli jiya Laraba a birnin Nairobi, inda shugabanni suka lashi takobin kawo karshen gurbatar muhalli.

Shugabannin kasashe da ministoci da 'yan kasuwa da jami'an MDD da wakilan kungiyoyin al'umma da masu rajin kare muhalli da taurari sama da 4,000 da suka halarci taron na yini 3, sun kuma amince da samar da jerin mafita tare da yin alkawarin inganta rayuwar biliyoyin mutane dake fadin duniya ta hanyar tsaftace iska da ruwa da kuma ban kasa.

A karon farko, ministocin muhalli sun bayar da sanarwa, suna masu kira ga kasashen duniya, su martaba kokarin karewa da magancewa da kuma takaita gurbatar iska da kasa da ruwa da tekuna, wadanda ke illa ga lafiya da al'umma da hallitu da tattalin arziki da kuma tsaro.

Ministocin sun kuma gabatar da kudure-kudure 13 da shawarwari 3 na magance matsalar gurbata tekuna da bazuwar sinadaran roba a muhalli, da karewa da rage gurbatar iska da cire sinadarin lead mai guba daga fenti da batura, da kare hallitun ruwa da tunkarar gurbatar ban kasa da kuma takaita gurbatar muhalli a yankunan dake fama da rikici da ta'addanci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China