in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaministan Sin ya yi kira da aka kara azama wajen tabbatar da kafuwar yankunan cinikayya cikin 'yanci na gwaji
2018-06-08 10:23:14 cri

Mataimakin firaministan Sin Hu Chunhua, ya yi kira da aka kara azama, wajen tabbatar da nasarar kafuwar yankunan cinikayya cikin 'yanci na gwaji da aka tsara samarwa a birnin Tianjin.

Hu Chunhua wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin ziyarar gani da ido da ya kai birnin na Tianjin, ya ce ya zama wajibi a gina yankin da kayayyaki masu nagarta, a kuma zakulo sabbin hanyoyin amfani da kwarewa, don cimma nasarar kara bude kofa da kasar ke yi ga kasashen ketare a dukkanin fannoni.

Hu, wanda kuma mamba ne a babbar hukuma mai lura da harkokin siyasa a kwamitin koli na JKS, ya jaddada bukatar amfani da kirkire kirkire, da dabarun kawar da matsaloli, tare da biyayya ga ka'idojin kasa da kasa yayin da ake gudanar da ayyuka.

Ya ce a watan da ya gabata, Sin ta fitar da sabbin tsare tsare, na kara zurfafa sauye sauye a yankin gwani na ciniki cikin 'yanci dake birnin Tianjin, da lardunan Guangdong da Fujian, a wani mataki na bunkasa aiwatar da sauye sauye, da kara bude kofa ga kasashen waje.

A ziyarar sa a Tianjin, Hu ya duba ofishin gudanarwa na tabbatar da kafuwar yankin Binhai dake birnin.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China