in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
2017: Darajar sayayya ta yanar gizo a Sin ta kai yuan tiriliyan 29.16
2018-05-29 21:09:58 cri

A shekarar 2017 da ta gabata, darajar sayayya ta yanar gizo da aka gudanar a kasar Sin ta kai yuan tiriliyan 29.16, wato kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.5, adadin da ya karu da kaso 11.7 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabace ta.

Hakan dai na kunshe ne cikin wani rahoto da ma'aikatar cinikayyar kasar ta Sin ta fitar a Talatar nan, yayin taro game da hada hadar cinikayya ta yanar gizo na bana da ya gudana a nan birnin Beijing. Rahoton ya kara da cewa, darajar hajojin da aka yi hada hadar cinikayyar su ta yanar gizo a shekarar ta bara ya kai yuan tiriliyan 16.87, adadin da ya karu da kaso 21 bisa dari sama da na shekarar da ta gabace ta, kana darajar hidimomi da aka bayar ta yanar gizo a shekarar ta 2017 ya kai yuan tiriliyan 4.96, adadin da ya karu da kaso 35.1 bisa dari, sama da na shekarar da ta gabace ta.

Da yake karin haske game da hakan, jami'in ofishin lura da hada hada ta yanar gizo da sarrafa bayanai a ma'aikatar cinikayyar ta Sin Qian Fangli, ya ce ana sa ran ganin karin ci gaba cikin sauri a wannan fanni a wannan shekara ta 2018. Qian Fangli ya ce ana kuma sa ran ganin fadadar hada hadar cinikayya ta yanar gizo, zuwa sauran yankunan kuda maso gabashin Asiya, da Afirka, da kuma latin Amurka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China