in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman Xi zai kai ziyara Amurka
2018-05-14 15:42:48 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Litinin cewa, manzon musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar Liu He zai kai ziyara Amurka daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Mayun da muke ciki don gudanar da tattaunawa kan harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Liu, mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin na JKS, kana shugaban tagawar kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, zai gudanar da wannan ziyara ce bisa gayyatar gwamnatin Amurka.

Bugu da kari, Liu zai tattauna da tawagar jami'an tattalin arzikin Amurka karkashin jagorancin sakataren baitul malin Amurka Steven Mnuchin kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China