in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da zagaye na biyu na taron baje kolin Guangzhou na 123
2018-04-24 13:24:30 cri

An kaddamar da zagaye na biyu na taron baje kolin birnin Guangzhou karo na 123 a jiya Litinin. Sakamakon kara ci gaban shawarar "Ziri daya da hanya daya", kamfanoni da masu sayayya su halarci wannan baje koli yadda ya kamata.

An kadamar da taron baje koli na Guangzhou a karon farko ne a shekarar 1957, kuma za a yi taron zagaye na biyu na wannan karo ne tsakanin ranekun 23 zuwa ranar 27 ga wata, inda za a nuna kayayyakin masarufi, da abubuwan kyauta, da abubuwan kayatar da gida da dai sauransu.

Daga cikin masu halartar taron, akwai kamfanoni 382 daga kasashe da yankuna 21 da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa, adadin da ya kai kashi 62 bisa dari, na dukkan kamfanonin ketare da ke halartar taron. Kayayyakin da aka nuna kuwa sun shafi dukkan fannonin shida.

An labarta cewa, ya zuwa yanzu, taron baje koli na Guangzhou ya riga ya rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin kai tare da hukumomin kasuwanci 46, da ke kasashe da yankuna 32 da shawarar ta shafa, bisa aniyar samar da hidimomi ga kamfanonin wadannan kasashen.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China