in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da bude kofa ga waje domin cimma moriyar juna
2018-04-28 09:41:06 cri

Jiya Jumma'a, tawagar zaunannun wakilai dake MDD da hukumar tattalin arziki da zaman takewar al'umma ta MDD sun kira taron karawa juna sani mai taken "Kiyaye tsari da ka'idojin ciniki tsakanin bangarori daban daban" a hedkwatar MDD dake birnin New York.

A yayin taron, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su goyi bayan ciniki tsakanin bangarori daban daban, yayin da kiyaye ka'idoji da tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban yadda ya kamata. Sa'an nan kuma, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga waje, ta yadda za a cimma moriyar juna.

Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, ana samun farfadowar tattalin arziki a fadin duniya, a sa'i daya kuma, ana gamu da matsalar kariyar ciniki da wasu kasashen duniya suka yi, lamarin da ya ba mu wahala wajen kiyaye yanayin zaman karko na tattalin arzikin duniya.

Haka zalika ya ce, ciniki tsakanin kasa da kasa shi ne muhimiyyar hanya gare mu wajen kawar da talauci da kuma neman ci gaba, wanda zai ba da babbar gudummawa wajen inganta dunkulewar kasa da kasa a fannin tattalin arziki da kuma samun dauwamammen ci gaban duniya.

Cikin shekaru 30 da suka gabata, adadin ciniki dake cikin ma'aunin tattalin arziki na GNP ya karu daga kashi 17 bisa dari na shekarar 1990 zuwa kashi 28 bisa dari a shekarar 2016, lamarin da ya nuna cewa, ciniki ya taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin duniya baki daya, wanda ya kuma ba da taimako ga mutane masu dimbin yawa wajen kawar da talauci, yayin da ciyar da mu'amalar dake tsakanin al'ummomin kasa da kasa gaba bisa fannonin tattalin arziki, zaman takewar al'umma da kuma al'adu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China