in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MOC: Har yanzu babu tattaunawa tsakanin Sin da Amurka kan takaddamar ciniki
2018-04-19 13:37:55 cri

Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin MOC ta sanar a yau Alhamis cewa, har yanzu ba a gudanar da wata tattaunawa ba tsakanin kasar Sin da Amurka dangane da batun takaddamar ciniki da ta kaure tsakanin manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya ba.

A ranar 17 ga watan nan na Afrilu ne Amurka ta mika bukata ga kungiyar ciniki ta duniya WTO, inda ta yi ikirarin cewa, tana son shiga tattaunawa tsakaninta da Sin domin dinke barakar da ta kunno game da kaddamar ciniki.

Matakin na Amurka ya biyo bayan ka'idojin kungiyar WTO ne, wadda ta baiwa mambobinta umarnin su gabatar mata da bukatar neman warware sabanin dake tsakaninsu cikin kwanaki 10, kamar yadda kakakin ma'aikatar ta MOC Gao Feng ya tabbatar da hakan.

Gao ya nanata cewa, matakin da kasar Amurka ta dauka na yin amfani da sashe na 232 da sashe na 301 na dokokinta ya ci karo da ka'idojin kungiyar WTO.

Gao ya ce, ya zuwa yanzu bangarorin biyu ba su gudanar da wata tattaunawa kan batun bincike bisa sashe na 301 na dokar Amurka ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China