in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gao Feng: "Ziri daya da hanya daya" riba ce ba nauyi ba ga kasashen da suka amince da shawarar
2018-06-08 10:02:28 cri

Kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Gao Feng, ya bayyana shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya", a matsayin tsarin da zai samarwa kasashen da suka amince da shi tarin alfanu, maimakon nauyin bashi da wasu ke zargin za a dorawa kasashen.

Da yake tsokaci kan hakan, a yayin wani taron manema labarai a jiya Alhamis, Gao Feng ya ce dukkanin ayyuka da ake gudanarwa karkashin tanajin shawarar, ana yin su ne bisa hadin gwiwar sassan dake da ruwa da tsaki domin cimma moriya ta bai daya.

Ya ce ci gaban shawarar na dogaro ne ga yanayin kamfanoni da kasuwanni, yayin da gwamnatoci ke samar da kyakkyawan yanayi na gudanar da hada hada bisa tsari.

Jami'in ya kara da cewa ya zuwa yanzu kamfanonin kasar Sin sun kafa huldodin tattalin arziki da cinikayya kusan 75, a kasashen waje daban daban karkashin shirin na "ziri daya da hanya daya", huldodin da suka kunshi jari da ya kai dalar Amurka biliyan 25.5, ya kuma samar da harajin da ya kai dala biliyan 1.7, tare da samar da ayyukan yi kusan 220,000 a kasashen da ake gudanar da su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China