in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fitar da rahoton shekara na shirin "ziri daya da hanya daya"
2018-03-26 10:01:47 cri

Jiya Lahadi madaba'ar wallafa littafin harkokin kasuwanci ta kasar Sin ta fitar da rahoton shekara na shirin "ziri daya da hanya daya" domin bayyana nasarorin da aka samu daga shirin na hadin gwiwa.

Babban editan rahoton, kuma shehun malami a kwalejin horas da jami'an JKS ta kwamitin tsakiya ta jam'iyyar wato Zhao Lei, ya ce shirin ya zama wata manufa da kasashen duniya suka amince da ita.

Wani jami'i sashen kula da harkokin kasashen waje na kwamitin tsakiya na JKS Jin Xin, ya ce rahoton ya ba da shawarwari kan samar da tsarin kare aukuwar haddura da kuma inganta sanya bukatun al'umma, wadanda za su tabbatar da aminci da ci gaban shirin yadda ya kamata.

Shirin na "ziri daya da hanya daya" na da nufin gina hanyar cinikayya da za ta hada nahiyoyin Asiya da Turai da Afrika a kan tsoffin hanyoyin siliki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China