in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron kara wa juna sani tsakanin kanana da matsakaitan kamfanoni kan zarafin zuba jari
2018-05-10 11:10:21 cri
A jiya Laraba, an gudanar da taron kara wa juna sani tsakanin kanana da matsakaitan kamfanoni, kan zarafin zuba jari bisa shawarar ziri daya da hanya daya. Cibiyar nazarin shawarar ziri daya da hanya daya ta masanan Sin da duniya ce ta shirya taron, inda aka tattauna batutuwan da suka fi jawo hankalin kamfanoni kanana da matsakaita, game da shawarar ziri daya da hanya daya, ciki har da cinikin ketare, da gine-gine, da kuma zuba jari.

A yayin da ake ta aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ayyukan gine-gine da kasar Sin ke gudanarwa sun samar da kuzarin bunkasa kasashen da ziri daya da hanya daya suka ratsa. Kanana da matsakaitan kamfanonin kasar Sin suna da fifiko na musamman ta fannin kirkire-kirkire, abin da ya sa suke da makoma mai kyau a kasuwannin kasashen. Taron ya fadakar da kamfanonin a kan dokokin kasashen da ziri daya da hanya daya suka ratsa, wanda kuma ya samar da wani dandalin hadin gwiwa gare su. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China